Jarin kai tsaye da bai shafi hada-hadar kudi ba da Sin ta zuba a ketare a rabin farkon bana ya kai dala biliyan 72.62
2024-07-25 20:38:16 CMG Hausa
Bisa alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar, daga watan Janairu zuwa watan Yunin bana, jarin kai tsaye wanda bai shafi hada-hadar kudi ba da kasar Sin ta zuba a kasashen waje a rabin farko na shekarar bana ya kai dalar Amurka biliyan 72.62, wanda ya karu da kashi 16.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.
Kazalika, jarin kai tsaye wanda bai shafi hada-hadar kudi ba da kamfanonin kasar Sin suka zuba a kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, ya kai dalar Amurka biliyan 15.46, wanda ya karu da kashi 9.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara. Kuma yawan kudaden shiga da kamfanonin Sin suka samu daga ayyukan gine-gine a kasashen dake cikin shawarar, ya kai dalar Amurka biliyan 58.92, wanda ya karu da kashi 0.7 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, kuma adadin kudaden sabbin kwangilolin da aka rattaba hannu a kansu ya kai dalar Amurka biliyan 93.35, wanda ya karu da kashi 18.5 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara. (Safiyah Ma)