logo

HAUSA

JKS ta yi taron nazarin rigakafin ambaliyar ruwa ayyukan agajin bala’i

2024-07-25 20:04:11 CMG Hausa

A yau Alhamis, zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ya gudanar da taron nazari da samar da rigakafin ambaliyar ruwa, da yaki da ambaliyar ruwa da ayyukan agajin bala’u. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS ne ya jagoranci taron.

Taron ya bayyana cewa, dole ne a ko da yaushe a sanya kare rayukan jama’a da tsaron lafiyarsu a gaba, da kara inganta hanyoyin sa ido, da inganta ba da gargadi da wuri, da karfafa alaka tsakanin gargadin farko da martanin gaggawa, da inganta saurin mayar da martani, da nuna fifikon tsaro, da sanya ido sosai daga tushe, da kuma fitar da mutanen da ke cikin hadari tun da wuri don rage asarar rayuka. (Yahaya)