logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da shugaban tawagar Fatah a shawarwari Mahmud Alul

2024-07-24 14:41:02 CMG Hausa

 

Kafin mabambantan bangarorin Palasdinu su kulla yarjejeniyar Beijing a jiya Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da Mahmud Alul, mataimakin shugaban Fatah, kana shugaban tawagar Fatah a shawarwarin. 

Wang Yi ya jaddada cewa, Sin na tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan halaltattun muradu Palasdinawa duk da fuskantar sauye-sauyen yanayin duniya. Ya ce rikicin Gaza ya haddasa bala’in jin kai, shi ya sa kasashen duniya suka sake mai da hankali kan wannan batun. Ya kara da cewa, daidaita wannan kuskure na bukatar a nace ga tsarin barin Palasdinawa sun jagoranta tare da aiwatar da harkokinsu da kansu. Kuma abin da aka sa a gaban komai shi ne, amfani da damammaki masu kyau don daidaita bambancin ra’ayi da kai wa ga matsaya daya da hanzarta dunkulewar al’umma da samun sulhu tsakaninsu bisa muradu masu tushe na Palasdinawa, ta yadda za a yi kokari tare wajen ingiza dakatar da bude wuta a Gaza, da samar da nagartaccen sharadi ga kafa kasar Palasdinu da Isra’ila.

A nasa bangare, Mahmud Alul ya gode da rawar da Sin take takawa wajen hanzarta mabambantan bangarori su samu sulhu a tsakaninsu. Yana mai cewa Palasdinu ba za ta manta da taimakon da Sin ta dade tana ba ta  cikin dimbin shekarun da suka gabata ba. Ya kara da cewa, Fatah za ta yi iyakacin kokarin ingiza mabambantan bangarori da su dunkule tare da sulhuntawa, ta yadda za su taka rawar gani wajen daidaita batun Palasdinu daga tushe. (Amina Xu)