Sin ta samu karuwar mafi yawan hatsi a yanayin zafi a cikin shekaru 9
2024-07-24 19:44:15 CMG Hausa
Han Jun, sakataren kwamitin JKS na ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta kasar Sin a yau Laraba ya ce, kasar Sin ta samu karuwar mafi yawan hatsi a yanayin zafi a cikin shekaru 9 da suka gabata, sakamakon yawan girbin alkama da aka samu.
Jami’in ya shaidawa taron manema labarai cewa, a bana an girbe kimanin gonar alkama kadada miliyan 23, wanda ya karu da kadada 31667 na yawan amfanin da aka samu a bara.
Yawan amfanin da aka samu a gonar kadada 0.07 na alkama ya karu da kilogiram 10, ko kuma kashi 2.6 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, wanda ke nuna babban ci gaba a cikin shekaru biyar da suka gabata, a cewar Han. (Yahaya)