Xi Jinping ya ba da amsar wasikar dukkan ma'aikatan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Xiamen
2024-07-24 19:18:09 CMG Hausa
A kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da amsar wasikar dukkan ma'aikatan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Xiamen na kasar Sin, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi kamfanin ya ci gaba da gudanar da kyakkyawar al'adarsa, da kokarin aiwatar da gyare-gyare, da kirkiro sabbin dabaru, ta yadda zai iya taka rawar gani a fannin taimakawa raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da inganta mu'ammala da hadin gwiwa tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. (Bello Wang)