logo

HAUSA

An bude dandalin baje koli na Sin da kudancin Asiya karo na 8

2024-07-23 16:10:49 CMG Hausa

 

A yau Talata an bude dandalin baje koli na Sin da kudancin Asiya karo na 8, wanda zai gudana a tsawon kwanaki 6 a birnin Kunming, hedkwatar lardin Yunnan.

Baje kolin ya samu halartar kasashe da yankuna, da kuma kungiyoyin kasa da kasa 82, inda kamfanoni fiye da 2000 suka baje hajojinsu, kuma rabi daga cikinsu kamfanoni ne masu jarin waje, wadanda suke shafar dukkanin kasashe dake kudancin Asiya da kudu maso gabashin Asiya. (Amina Xu)