logo

HAUSA

Wang Yi: PLO ita ce kadai halatacciyar wakiliyar al’ummar Falasdinu

2024-07-23 19:26:25 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a yau Talata cewa, babban sakamakon tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinawa da aka gudanar a birnin Beijing, shi ne an tabbatar da cewa, kungiyar ‘yantar da Falasdinu Wato PLO ita ce kadai halaltacciyar wakiliyar al’ummar Falasdinu.

Wang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a yayin bikin rufe tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinawa. Ya kuma shaida rattaba hannu kan sanarwar kawo karshen rarrabuwar kawuna da karfafa hadin kai da bangarorin Falasdinawa 14 suka yi. (Yahaya)