Li Qiang ya taya murna ga Ursula von der Leyen game da sake zabarta a matsayin shugabar hukumar EU
2024-07-23 19:40:50 CMG Hausa
A yau ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya aike da sakon taya murna ga Ursula von der Leyen game da sake zabarta a matsayin shugabar hukumar kungiyar Tarayyar Turai.
Li Qiang ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kungiyar EU don ci gaba da karfafa tushen siyasa na dangantakar dake tsakanin Sin da EU, da mayar da martani tare ga kalubalen da duniya ke fuskanta, da ba da gudummawa sosai wajen kyautata jin dadin jama'ar bangarorin biyu, da kiyaye zaman lafiyar duniya da wadata. (Yahaya)