Wang Yi ya jaddadawa manyan jami’an USCBC aniyar Sin ta zurfafa gyare-gyare da kara bude kofa ga kasashen waje
2024-07-23 10:29:02 CMG Hausa
Ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da tawagar manyan jami’an majalissar gudanarwar kungiyar ’yan kasuwar Amurka da Sin ta USCBC a jiya Litinin a Beijing.
Manyan jami’an dai sun iso kasar Sin ne domin gudanar da ziyarar aiki ta mako guda, don kara fahimtar ma’anar cikakken zama na 3 na kwamitin kolin JKS na 20 da aka kammala a kwanakin baya.
Yayin zantawarsu, Wang wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya jaddada matsayar kasar Sin don gane da kara zurfafa sauye sauye daga dukkanin fannoni, da ingiza zamanantarwa irin ta Sin.
Ministan ya ce alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci a kawancen kasashe biyu na duniya, don haka ake fatan ’yan kasuwar Amurka za su ci gaba da aiki kafada da kafada da bangaren Sin, ba kawai don cimma manyan sakamakon bunkasuwa ba, har ma da samar da sabbin gudummawar raya ci gaban alakar kasashen biyu, da kawancen dake tsakanin al’ummun su.
A nasu bangaren kuwa, jami’an tawagar ta USCBC, sun ce hadakarsu za ta tabbatar da ingiza sabon zagayen sauye-sauyen tattalin arziki, da bude kofa a kasar Sin, da kuma jawo jarin waje mafi dacewa.
Kaza lika, ’yan kasuwar na Amurka sun ce suna da kwarin gwiwa game da ci gaban hadin gwiwa tare da Sin, kana suna fatan kara zurfafa hadin gwiwar sassan biyu a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da samar da ci gaba maras gurbata muhalli, da kiwon lafiya, da ilimi, da musaya tsakanin al’ummun sassan biyu. (Saminu Alhassan)