logo

HAUSA

Sin tana dora muhimmanci kan dangantakar abokantaka ta gargajiya da Rwanda

2024-07-23 20:29:01 CMG Hausa

 

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum yau Talata.

Dangane da sakamakon babban zaben kasar Rwanda, Mao Ning ta ce, shugaba Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga shugaba Paul Kagame ta hanyar diplomasiyya, bisa sake zabarsa a matsayin shugaban kasar. A ko da yaushe kasar Sin tana mutunta dangantakar abokantaka ta gargajiya tsakaninta da kasar Rwanda, kuma tana son yin hadin gwiwa da kasar Rwanda wajen zurfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban.

Dangane da taron shirya babban taron bita kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya da ke gudana a birnin Geneva, Mao Ning ta bayyana cewa, babbar manufar kasar Sin ta shiga wannan taro ita ce, ya kamata kasashe masu mallakar makaman nukiliya su mai da martani game da damuwa da bukatu na kasashen da ba su da makaman nukiliya, da kuma kulla yarjejeniya cewa ba za a zama na farkon yin amfani da makaman nukiliya kan juna ba ko fitar da wata sanarwar siyasa.

Kan tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinu da kasar Sin ta shirya, Mao Ning ta bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da bangarorin Falasdinu 14 suka hallarta a nan birnin Beijing, domin gudanar da shawarwarin sulhu, wanda ya kawo kyakkyawar fata ga al'ummar Falasdinu dake cikin wahala.

Dangane da Amurka ta sayar da makamai ga yankin Taiwan, Mao Ning ta ce, lamarin ya keta manufar kasar Sin daya tak, da kuma yarjejeniyoyi guda uku da Sin da Amurka suka daddale, Sin na adawa da hakan sosai.

Game da rikicin kasar Ukraine, Mao Ning ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan zaman lafiya da tattaunawa, tare da nuna goyon baya ga al'ummomin kasa da kasa wajen samun karin fahimtar juna, da kuma neman hanyoyin da za a bi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa. (Safiyah Ma)