logo

HAUSA

Wakilin Sin kan harkokin yankin Gabas ta Tsakiya ya tattauna ta wayar tarho da wakilin EU

2024-07-23 21:26:01 CMG Hausa

A ranar 23 ga watan Yulin 2024, wakilin gwamnatin Sin na musamman kan harkokin yankin Gabas ta Tsakiya Zhai Jun ya tattauna ta wayar tarho da wakilin musamman na EU kan shirin zaman lafiya na yankin Gabas ta Tsakiya Sven Koopmans bisa bukatarsa.

Koopmans ya yaba ya kuma taya kasar Sin murnar samun nasarar shiga tsakanin bangarorin Falasdinawa 14 a kasar Sin don yin tattaunawar sulhu da kuma rattaba hannu tare kan “Sanarwar Beijing kan kawo karshen rarrabuwar kawuna da karfafa hadin kan Falasdinawa”. Yana mai jaddada cewa, wannan babbar nasara ce.

A nasa bangare, Zhai Jun ya ce, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kungiyar tarayyar Turai EU, domin sa kaimi ga tsagaita bude wuta a zirin Gaza, da cimma cikakkiyar adalci da dawwamamman maslaha kan batun Falasdinu. (Yahaya)