Yawan tikitin kallon fina-finan lokacin zafi da aka sayar ya zarce dalar miliyan 841
2024-07-22 16:07:54 CMG Hausa
Ya zuwa tsakar ranar yau Litinin, yawan tikitin fina-finan da aka gabatar a lokacin zafi na shekarar 2024 a nan kasar Sin, wanda aka sayar ya zarce dala miliyan 841, daga cikinsu fina-finai 3 dake sahun gaba kamfanonin Sin suka gabatar da su.
Lokacin hutu na zafi shi ne na gabatar da fina-finai mafi tsawo cikin duk shekara a fannin nuna fina-finai a babban yankin Sin. A lokacin hutu na zafi na shekarar 2023, yawan kudin tikitin fina-finai da aka sayar ya kai kudin Sin yuan biliyan 20.6, kwatankwacin wajen dalar Amurka biliyan 2.88. (Amina Xu)