Xi ya bukaci a yi azamar aiwatar da dukkanin matakan ceto bayan karyewar wata gada a arewa maso yammacin kasar Sin
2024-07-20 16:17:30 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci da a kara azama wajen aiwatar da dukkanin matakan ceto, da samar da agajin jin kai, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sakamakon karyewar wata gada mai dauke da babbar hanyar motoci a lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin.
A cewar hukumomin wurin, gadar ta karye ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya raunata ta, kuma ya zuwa safiyar Asabar din nan, an tabbatar da rasuwar mutane 12 sakamakon ibtila’in, kana ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto bayan samun rahotannin bacewar kimanin mutane 31. (Saminu Alhassan)