logo

HAUSA

Firaministan kasar tsibiran Solomon: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ta sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin kasar

2024-07-20 20:06:44 CMG Hausa

Kasar tsibiran Solomon na kudu maso yammacin tekun Pasifik, wadda take da tsibirai fiye da 900. Bayan da Jeremiah Manele ya hau kujerar firaministan kasar, ya taba bayyana cewa, a cikin shirin raya tattalin arzikin kasar da sabuwar gwamnatinsa ta gabatar, sa kaimi ga gina ababen more rayuwa shi ne mafi muhimmanci.

Kaza lika, yayin da firaminista Manele ya zanta da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta kasance abokiyar hadin gwiwa mafi girma ga kasarsa a fannin gina ababen more rayuwa. Ya ce raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya na da muhimmanci sosai ga kasar tsibiran Solomon. Bisa shawarar, kasar Sin ta aiwatar da wasu ayyukan taimakawa kasar tsibiran Solomon.

A kwanakin baya, kasashen biyu sun daddale sabbin yarjejeniyoyin hadin gwiwa, wadanda suka taimaka wajen hade ayyukan raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, da manufofin raya kasar tsibiran Solomon na tsakanin shekarar 2016 zuwa ta 2035. (Zainab Zhang)