Sin na matukar adawa da shigar Japan atisayen soji na hadin gwiwa da yankin Taiwan
2024-07-19 19:56:28 CMG Hausa
Kasar Sin ta bayyana matukar rashin jin dadi, da adawa da shigar kasar Japan atisayen baya-bayan nan na sojojin ruwa, na hadin gwiwa tare da yankin Taiwan na Sin, ta kuma gabatar da korafi mai karfi ga bangaren na Japan.
Da yake tabbatar da hakan a Juma’ar nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin ta bukaci Japan da ta nacewa manufar nan ta Sin daya tak a duniya, da batutuwan da sassan biyu suka amince, cikin takardun bayanan siyasarsu guda 4, kana Japan din ta gaggauta gyara kura-kuranta, ta kauracewa amincewa, da goyon bayan ‘yan aware masu "Neman ‘yancin Taiwan" daga dukkanin fannoni.
Kaza lika, Sin na fatan Japan za ta yi taka-tsantsan a furuci da ayyukanta, don gane da batutuwan da suka shafi gabashi da kudancin tekun Sin, ta kuma kauracewa illata yanayin zaman lafiya da daidaito a mashigin tekun Taiwan, da kuma alakar Sin da Japan. (Saminu Alhassan)