Bude kofofin kasar Sin muhimmin mataki ne na ingiza ci gaba da wadatar duniya
2024-07-19 21:02:09 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce bude kofofin kasar Sin muhimmin mataki ne na ingiza ci gaba da wadatar dukkanin duniya. Lin Jian ya bayyana hakan ne a yau Juma’a, yayin taron manema labarai da ya jagoranta.
Ya ce daga kafuwar yankunan gwaji na gudanar da cinikayya cikin ‘yanci guda 22, da gina tashar ruwa ta gudanar da cinikayya maras shinge ta Hainan, zuwa sanya hannu, da aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa ta raya tattalin arzikin shiyya wato RCEP, da kafa tsarin yankunan gudanar da cinikayya cikin ‘yanci masu inganci na kasa da kasa, daga ci gaba da rage jerin sassan da ba a yarda a zuba jarin waje cikinsu ba, zuwa rangwame ga masana’antun samar da hidimomi, irinsu na sadarwa, da hidimomin kiwon lafiya, daga yayata hadin gwiwar gina shawarar Ziri Daya da Hanya Daya mai inganci, zuwa gina dandalin hadin gwiwar raya tattalin arzikin kasa da kasa, da cinikayya, irinsu baje kolin shigo da hajoji, da baje kolin hada-hadar bayar da hidima, da na kayayyakin sayayya, ana ta aiwatar da manyan matakai na fadada kara bude kofa a matsayin koli, ba wai kawai a matsayin gajiyar da sassan kasa da kasa suke samu daga ci gaban kasar Sin kadai ba ne, har ma hakan matsaya ce da duniya ta amince da ita, don gane da kyakkyawan fata game da bunkasar kasar Sin.
Lin Jian ya kara da cewa, sanarwar bayan taron da aka fitar, yayin da aka kawo karshen cikakken zama na 3 na kwamitin kolin JKS na 20, ta yi nuni da yadda batun bude kofar kasar Sin ke zama alamar zamanantarwa irin ta Sin. Sin za ta ci gaba da zurfafa sauye-sauye, da kara bude kofa sosai ga sauran sassan kasa da kasa, kana za ta mayar da babbar kasuwarta wata dama mai fadi ga duniya. Kaza lika, za ta ci gaba da yayata salon zamanantarwa irin ta Sin, ta hanyar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, tare da shigar da sabon karfi ga cimma nasarar zamanantarwa irin ta kasa da kasa tare da salon zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Saminu Alhassan)