logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya fitar da sabon nau'in karafan kafafun jiragen kasa masu saurin tafiya

2024-07-18 13:48:16 CMG Hausa

Wani reshen kamfanin CRRC, babban kamfanin kera jiragen kasa na kasar Sin, a jiya Laraba ya fitar da wani sabon nau'in karafan kafafun jiragen kasa ko chassis wadanda za a yi amfani da su a jiragen kasa masu saurin tafiya masu tafiyar kilomita 400 cikin sa'a guda.

Idan aka kwatanta da nau’in chassis da aka dora a waje, nauyin wannan sabon chassis din ya ragu da kashi 20 cikin dari. Zai iya rage yawan makamashin da jirgin kasa ke amfani da shi da kashi 15 cikin dari, sannan kuma zai iya rage saurin cinyewar kafafun jirgin kasa da kusan kashi 30 cikin dari, kana zai rage farashin kula da layukan dogo da chassis da kashi 15 cikin dari a duk tsawon aikinsa, wanda hakan zai sa jiragen kasa na lantarki (EMU) kara kiyaye muhalli da kara tsimin makamashi, a cewar makerin wato kamfanin taragun jiragen kasa na CRRC Changchun.

Karafan kafafun layin dogo muhimmin sashi ne na jirgin kasa. Suna daukar nauyin jirgin, suna amfani da kafafu wajen ba da jagoranci a kan layuka da kuma kasancewa matashi wajen rage tasirin girgizar da a kan samu yayin da jirgin kasa ke tafiya. (Yahaya)