logo

HAUSA

Sin Ta Soki Lamirin Bayanan Vietnam Game Da Iyakarta Ta Karkashin Tekun Kudancin Sin

2024-07-18 19:49:07 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da bayanan da kasar Vietnam ta gabatarwa hukumar MDD, mai lura da batutuwan shata iyakar yankunan teku ko UNCLCS, game da iyakar Vietnam din ta karkashin tekun kudancin Sin.

Da yake tabbatar da hakan a Alhamis din nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya ce matsayar Vietnam din ta shafi mamayar tsibiran Nansha na Sin, da keta hurumin mulkin yankunan Sin, da hakkoki da moriyar kasar Sin. Kaza lika, hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa, ciki har da na MDD, da na taron MDD game da dokokin teku, kana ya sabawa ka’idojin da ake bi wajen warware sabani game da iyakokin teku tsakanin Sin da Vietnam, da ma yarjejeniya mai nasaba da yadda sassan yankunan dake kewaye da tekun kudancin Sin za su sulhunta tsakaninsu, wadda Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN ciki har da Vietnam suka rattabawa hannu.  (Saminu Alhassan)