logo

HAUSA

Ministan Ghana: AfCFTA za ta iya bunkasa masana'antar man fetur a Afirka

2024-07-18 09:52:35 CMG Hausa

Karamin minista a ma’aikatar makamashi ta kasar Ghana Herbert Krapa, ya bayyana a ranar Laraba cewa, yankin cinikayya maras shinge na nahiyar Afirka wato AfCFTA na da damar bunkasa masana'antar dake shafar man fetur a nahiyar.

Ministan ya bayyana hakan ne a jawabinsa a taron man fetur na kasa da kasa na Ghana da aka bude a Accra, babban birnin kasar, inda ya bukaci kasashen Afirka da su bunkasa masana'antar don samun damar biyan bukatun man fetur a nahiyar tare da samun moriya daga kyakkyawar tsarin samarwa na masana’antar.

Krapa ya ce, “AfCFTA na iya inganta hanyoyin samun kasuwa, da karfafa zuba jari, da kuma bunkasa tattalin arziki. Dole ne mu yi amfani da wadannan damammaki don karfafa masana'antunmu da inganta ci gaba mai dorewa a fadin nahiyar.”

Domin masana'antar man fetur ta nahiyar ta samu cikakkiyar moriyar AfCFTA, ministan ya ce tilas ne masana'antar ta yi hange fiye da yadda ta  saba cin kasuwa, ta kuma fadada kayayyakin da ake da su. (Yahaya)