logo

HAUSA

Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Dukkanin Sassa Da Nufin Daga Martabar BRI Zuwa Babban Matsayi

2024-07-18 20:07:36 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki da dukkanin sassa wajen taimakawa juna, da aiki tare, domin ingiza ci gaban shawarar Ziri Daya da Hanya Daya wato BRI zuwa sabon matsayi da inganci.

Lin Jian, ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da ya jagoranta, lokacin da yake amsa tambayoyi game da ci gaba, da nasarorin baya-bayan nan da shawarar BRI ta samu, yana mai cewa cikin shekaru fiye da 10 da suka shude, Sin ta sanya hannu kan takardun hadin gwiwa masu nasaba da shawarar tsakaninta da sama da kasashen duniya 150, da sama da hukumomin kasa da kasa 30.

A shekarar bara, cinikayyar hajoji tsakanin Sin da kasashe abokan tafiyarta ta kai darajar yuan tiriliyan 19.5, adadin da ya karu da kaso 2.8%, kuma ya kai kaso 46.6% cikin jimillar hada-hadar shige da ficen hajoji da kasar ta gudanar, wanda ya kai matsayin koli a yawa da kima, tun bayan gabatar da shawarar ta Ziri Daya da Hanya Daya. (Saminu Alhassan)