logo

HAUSA

Sin za ta tallafawa masana’antun gida da na waje a fannin sabunta na’urori da yin musayar tsoffin kaya da sabbi

2024-07-17 21:22:36 CMG Hausa

A yau Laraba ne ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki, game da fayyace manufar nan ta daga matsayi, da sauya na’urorin gudanar da ayyukan masana’antu, da maye gurbin tsoffin hajojin da al’umma ke amfani da su da sabbi.

Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin ministan cinikayya, kuma mataimakin wakilin kasar Sin a fannin shawarwarin cinikayya na kasa da kasa Ling Ji, ya ce manufar sabunta kayan aiki, da maye gurbin kayayyakin da al’umma ke amfani da su da sabbi, za ta samar da zarafin fadada sayayya a cikin gida, da ingiza zuba jari, da daga mizanin sayayya, da samar da babbar kasuwa ga dukkanin nau’o’in kamfanoni, ciki har da masu jarin waje.

Jami’in ya kara da cewa, ana fatan kamfanonin waje za su yi amfani da wannan dama wajen zurfafa cin gajiya daga kasuwannin Sin, tare da fadada zuba jarinsu a kasar ta Sin.  (Saminu Alhassan)