logo

HAUSA

Sin ta bukaci WTO ta kafa kwamiti don gane da takkadama kan dokar rage hauhawar farashi ta Amurka

2024-07-16 10:16:42 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi kira ga hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, ta kafa wani kwamitin kwararru don gane da batun tallafin ababen hawa masu amfani da lantarki dake karkashin dokar rage hauhawar farashin kayayyaki ta Amurka.

Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce domin kare muradu da hakkokin masana’antar ababen hawa masu amfani da lantarki, a ranar 26 ga watan Maris, kasar Sin ta shigar da kara gaban sashen warware takkadama ta WTO, don gane da tallafin Amurka kan ababen hawa masu amfani da lantarki. Sai dai bangaren Amurka ya gaza cimma masalaha da kasar Sin ta hanyar tuntubar juna, wanda shi ne dalilin Sin na daukaka batun.

A cewar ma’aikatar, dokar ta ba kayayyakin da suka fito daga wasu zababbun yankuna kamar Amurka, matsayin wadanda suka cancanci tallafi, ta kuma ware kayayyaki daga mambobin WTO, ciki har da Sin, sannan ta kafa shingaye da kawo tsaiko ga kokarin da ake yi na komawa ga amfani da kayayyaki masu kare muhalli.

Kasar Sin ta shirya daukaka kara da daukar kwararan matakai domin daukaka iko da ingancin tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa karkashin jagorancin WTO, da kuma kare kokarin da sassan duniya ke yi cikin hadin gwiwa na yaki da sauyin yanayi. (Fa’iza Mustapha)