Qiushi za ta wallafa mukalar Xi mai taken “Dole ne mu nace cikin kwarin gwiwa da ‘yanci”
2024-07-15 15:57:22 CMG Hausa
Mujallar Qiushi ta 14, za ta wallafa wata muhimmiyar mukalar shugaban kasar Sin Xi Jinping mai taken “Dole ne mu nace cikin kwarin gwiwa da ‘yanci” gobe Talata 16 ga wannan wata.
Mukalar ta bayyana cewa, kwarin gwiwa na da matukar muhimmanci wajen raya kai. Kuma wayewar kan kasar Sin ta shafe tsawon dubban shekaru ba tare da tsayawa ba. Wannan ita ce al’ajabin wayewar kan dan adam da ma kwarin gwiwarsa.
A cewar mukalar, idan babu kwarin gwiwa mai karfi a kowanne bangare, ba zai yiwu a samu karfin halin zurfafa gyare-gyare ba. Haka kuma, idan babu gyare-gyare, to ba za a samu kwarin gwiwa mai dorewa yadda ya kamata ba.
Ya ce za su zurfafa gyare-gyare domin kara kyautata tsarin gurguzu mai sigar musammam ta kasar Sin, da nufin samun kwarin gwiwa kan tsarin, ba wai a saki jiki ba, sai dai ma ci gaba da kawar da matsaloli ta yadda za a samu ingantuwa da dorewar tsarin. (Fa’iza Mustapha)