logo

HAUSA

Sin ta jinjinawa kyawawan kalaman zababben shugaban Iran don gane da alakar sassan biyu

2024-07-15 20:01:49 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin ta yi maraba da kyawawan kalaman zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, don gane da kyakkyawar alakar sassan biyu, kuma Sin din a shirye take ta yi aiki da sabuwar gwamnatin Iran, wajen ingiza ci gaba na tsawon lokaci bisa daidaito, na cikakkiyar dangantakar kasashen biyu daga dukkanin fannoni.

Lin Jian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce wasu rahotanni sun nuna yadda sabon zababben shugaban na Iran ya rubuta wata makala da ya sanyawa hannu mai nasaba da harkokin wajen kasar, kuma aka wallafa jaridar “Tehran Times”, inda a cikinta ya ce, Iran na mutunta kawancen gargajiya tsakaninta da Sin, yana kuma fatan zurfafa hadin gwiwa da Sin a kan tafarkin gina sabon tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa. Kaza lika ya jinjinawa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa, wajen ingiza kyautatuwar alakar Iran da kasar Saudiyya.   (Saminu Alhassan)