logo

HAUSA

An kaddamar da harkar sada zumunta a tsakanin yaran Sin da na Afirka

2024-07-14 20:39:49 CMG Hausa

An shirya bikin maraba da wadanda suka halarci harkar sada zumunta tsakanin yaran Sin da na nahiyar Afirka a cibiyar yara ta kasar Sin a yau Lahadi, inda yara 35 daga kasashen Namibia, da Afirka ta Kudu, da Somaliya, da Uganda, da Afirka ta Tsakiya, da iyayensu suka taru da yaran kasar Sin.

Yayin bikin, yaran Sin da na Afirka sun karawa juna fahimta ta hanyar wasanni, kana sun gabatar da shirye-shiryen raye-raye da wasan Kungfu da sauransu. Yaran sun yi zane-zane tare kan wata doguwar takarda, don nuna zumunta a tsakaninsu.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da hukumar hadin gwiwa ta mata ta kasar Sin ne suka karbi bakuncin gudanar da harkar, kana cibiyar yara ta kasar Sin ta ba da taimako. A kwanaki shida masu zuwa, yaran za su kai ziyara fadar sarakuna ta Sin wato Forbidden City a Beijing, da gidan adana kayayyakin kimiyya da fasaha na lardin Henan, da gidan adana kayan tarihi na Rawayen kogi da sauransu, don kara sada zumunta ta hanyar yin karatu da mu’amala da juna. (Zainab Zhang)