Sin ta fitar da sanarwa game da dagewar da Amurka ta yi na amincewa da rattaba hannu kan abin da ake kira "kudirin da ya shafi Xizang"
2024-07-13 17:38:37 CMG Hausa
Yau Asabar, kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya fitar da wata sanarwa, inda ya yi kakkausar suka kan dagewar da Amurka ta yi, ta amincewa gami da rattaba hannu kan abin da ake kira "kudirin da ya shafi Xizang".
Sanarwar ta bayyana cewa, Xizang wani yanki ne mai tsarki na kasar Sin da ba zai iya ballewa ba. Kuma harkokin Xizang, na cikin gidan kasar Sin ne, kana babu wani bangaren waje da zai iya tsoma baki a ciki.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, a halin yanzu, Xizang na cikin mafi kyawun lokaci a tarihinsa, ta fuskar samun ci gaba mai dorewa, kuma babu wani mutum da wani karfi da zai yi nasara a yunkurinsa na kawo cikas ga al'ummomin Xizang a kokarin da suke yi na samun ingantacciyar rayuwa.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, idan har Amurka ta nace kan amincewa da rattaba hannu kan kudirin, Sin za ta dauki kwararan matakai bisa doka don tabbatar da ikonta na kiyaye mulkin kai da tsaro, da kuma samun ci gaba. (Bilkisu Xin)