logo

HAUSA

Kasar Sin ta shirya bunkasa ci gaban duniya na bai daya

2024-07-13 17:38:32 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya ce Kasarsa za ta yi amfani da dabarunta na zamantar da kanta tare da inganta samar da ci gaba na bai daya a duniya.

Wang Yi ya bayyana haka ne cikin jawabin da ya gabatar na bikin bude taron manyan jami’ai karo na 2 na Dandalin Tattaunawar Yunkurin Duniya na Samar da Ci Gaba na Bai Daya, wanda aka yi jiya Juma’a a Beijing.

A cewarsa, tun bayan da Sin ta gabatar da shawarar raya duniya ta GDI kusan shekaru 3 da suka gabata, hadin kai karkashinta na ci gaba da karfafa tare da samar da kyawawan sakamako, lamarin dake samun yabo da karbuwa daga kasa da kasa, yana mai cewa, Sin na mayar da hankali kan hakikanin bukatun jama’ar dukkan kasashe da zurfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa da karfafa daidaita manufofin neman ci gaba tsakanin dukkan bangarori.

Wang Yi ya kuma gana da takwaransa na Gabon Regis Onanga Ndiaye da ta Madagascar, Rafaravavitafika Rasata da tsohon sakatare janar na MDD Ban ki-moon, wadanda suka halarci bikin bude taron a jiya. (Fa’iza Mustapha)