Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta CGTN ta nuna amincewar jama'ar da sauye sauyen da Sin ke aiwatarwa
2024-07-11 15:54:22 CMG Hausa
Taro na uku na zaman kwamitin kolin JKS na 20 dake tafe na ci gaba da jan hankalin sassan kasa da kasa. Kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa sauye sauye daga dukkanin fannoni, da mayar da hankali ga yayata zamanantarwa irin ta Sin.
Game da hakan, sakamakon wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 76.9 bisa dari na wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu, sun jinjinawa nasarar da Sin ta cimma a fannin samar da ci gaba mai inganci, kana suna fatan kara fadadar zurfafa sauye sauyen na Sin daga dukkanin fannoni zai samar da karin damammaki ga sassan duniya.
Tun bayan babban taron JKS na 18, an aiwatar da manufofin sauye sauye da suka haura 2,000, wadanda suka shafi sassa daban daban na tattalin arziki, siyasa, raya al’adu, kyautata zamantakewa da kare muhallin halittu.
Yayin kuri'un na jin ra'ayin jama'a, kaso 80.3 bisa dari na masu bayyana ra'ayoyinsu sun bayyana gamsuwa da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, suna masu imani da cewa hakan zai haifar da karin alfanu ga duniya baki daya. Yayin da kaso 93.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayin suka jinjinawa karfin kwazon Sin a fannin raya ilimin kimiyya da fasaha. Sai kuma kaso 85.4 bisa dari da suka yabi nasarar da Sin ta samu ta fuskar kirkire-kirkire na kashin kai. Baya ga kaso 78.5 bisa dari da suka amince cewa, sassan masana’antu dake amfani da makamashi mai tsafta za su kara ingiza ci gaba mai inganci na kasar Sin.
Masu bayyana ra'ayoyi 15,037 daga sassa daban daban na duniya ne suka bayyana matsayarsu, ciki har da al’ummun kasashe masu sukuni da suka hada da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Sifaniya da Australia, da kuma wasu kasashe masu tasowa irin su Brazil, da Thailand, hadaddiyar daular Larabawa, da Masar da Afirka ta Kudu. (Saminu Alhassan)