logo

HAUSA

An kaddamar da dandalin tattaunawa na Nishan kan wayewar kan duniya a lardin Shandong na kasar Sin

2024-07-10 21:11:57 CMG Hausa

An kaddamar da dandalin tattaunawa na Nishan kan wayewar kan sassan kasa da kasa karo na 10 a birnin Qufu dake lardin Shandong na kasar Sin yau Laraba 10 ga wata. An dai shirya dandalin nan, mai taken “al’adun gargajiya da wayewar kai ta zamanin yau”, da nufin aiwatar da shawarar wayewar kai ta duniya a zahirance, da tallata akidun daukacin bil’adama na bai daya, tare da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Dandalin Nishan na nuna himma da kwazo, wajen inganta mu’amala tsakanin kasashe da kabilu da al’adu iri daban-daban, da maida hankali kan muhimman batutuwan da suka jawo hankalin gida da na waje, don neman dabaru da mafita, ga shawo kan kalubalolin duniya, da raya wayewar kan bil’adama a duniya. (Murtala Zhang)