A karon farko na’urar hakar ma’adinai a karkashin teku ta Sin ta gudanar da aikin gwaji a wuri mai zurfin mita fiye da 4000
2024-07-09 13:59:41 CMG Hausa
Aikin nazarin muhimmiyar fasaha da na’urorin hakar ma’adinai na karkashin teku mai zurfi da kasar Sin ke gudanarwa na samun babban ci gaba, kamar dai yadda gwamnatin birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin ta bayyana hakan a gun wani taron manema labarai da ya gudana a kwanan baya.
An ce, wata na’urar gwaji mai aiki a kasan teku mai zurfi, wadda jami’ar Jiao Tong ta Shanghai ta yi nazari da kuma kera mai lakabin “Pioneer 2”, ta cimma nasarar aikin gwaji a teku. Sau 5 a jere, na’urar ta yi nutso cikin teku mai zurfi da tattara ma’adinai da dama, matakin da ya alamta cewa, a karon farko an yi aikin gwajin na’urar a teku mai zurfin da ya kai fiye da mita 4000, har ma wani lokaci ya kai mita 4,102.8. (Amina Xu)