logo

HAUSA

Jami’an Sin da Habasha sun yi kira ga samun jituwa tsakanin mabambantan al’ummu domin samar da zaman lafiya a duniya

2024-07-08 10:27:24 CMG Hausa

Jami’an Sin da Habasha sun nanata bukatar girmamawa da rungumar bambance-bambancen dake akwai tsakanin al’ummu, domin inganta zaman lafiya da jituwa da fahimta tsakanin mutane da kuma samun ci gaba a duniya.

An yi kiran ne yayin wani taron tattaunawa na manyan jami’an kasashen biyu, mai taken “Jerin Lakca kan Mabanbantan Al’ummu”, wanda ya gudana ranar Asabar, a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Manufar taron ita ce, kara karfafa musaya da hadin kai tsakanin kungiyoyin al’umma na Sin da Habasha.

Da yake jawabi yayin taron, mataimakin shugaban kungiyar inganta musaya tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin mai zaman kanta, Li Jun, ya ce yana da muhimmanci a daukaka ka’idojin hulda tsakanin mutane, domin samun zaman jituwa tsakanin mabambantan al’ummun duniya. 

A cewarsa, gwamnatin kasar Sin na nacewa wajen goyon bayan kokarin da mutanen Habasha da sauran kasashe suke yi na gado da raya al’adunsu, yayin da suke kuma zabarwa kansu hanyar ci gaba da ta dace da kasashensu. Ya ce a shirye kasar Sin take ta ci gaba da tattaunawa kan jituwa tsakanin mabambantan al’ummu da musayar al’adu da dabarun shugabanci. (Fa’iza Msutapha)