Yankin Asia da Pacific ba ya bukatar wani gungun dakarun soji
2024-07-08 19:56:34 CMG
A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, yankin Asia da tekun Pacific baya bukatar wani gungu na sojoji, ko wani karamin rukunin da ka iya rura wutar fito-na-fito tsakanin sassa daban daban, da ingiza sabon salon yakin cacar baka.
Lin Jian, ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga yarjejeniyar tsaro da bangarorin Japan da Philippines suka sanyawa hannu a yau din, wadda ta tanadi baiwa sassan biyu damar jibge sojoji a yankunan junan su.
Jami’in ya kara da cewa, bai kamata musaya da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta gurgunta fahimta da amincewa da juna tsakanin kasashen dake yankin ba, kana hakan bai kamata ya zama wani zarafi na lalata zaman lafiya da daidaito a yankin ba, kana bai dace ya kasance damar illata wani bangare, ko gurgunta moriyar wani sashe na daban ba.
Dangane da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, na goyon bayan yunkurin kare harshe, da addini da al’adun gargajiya, har da ikon zabar shugabannin addini a yankin Xizang, Lin Jian ya ce Sin na fatan Amurka za ta fahimci muhimmanci da hadarin tsoma baki cikin batun yankin Xizang, ta kuma dakatar da goyon bayan duk wasu sassan ‘yan aware masu burin "’yantar da Xizang" daga aiwatar da matakan kin jinin kasar Sin. (Saminu Alhassan)