logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Tajikistan sun halarci bikin kammala aikin gina wasu manyan gine-gine

2024-07-06 15:04:02 CMG Hausa

A ranar Juma'a bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Tajikistan Emomali Rahmon, sun halarci bikin kammala aikin gina ginin majalissar dokokin kasar Tajikistan, da na gwamnatin kasar, da kasar Sin ta ba da tallafinsu, a birnin Dushanbe, fadar mulkin kasar Tajikistan.

A wurin bikin, shugaba Xi na kasar Sin ya taya murnar kammala aikin gina wadannan manyan gine-ginen 2, da nuna jinjina da godiya ga ma'aikata masu aikin ginin na kasashen Sin da Tajikistan, wadanda suka yi hadin gwiwa wajen kammala aikin ginin yadda ake bukata.

A nasa bangare, shugaba Rahmon na kasar Tajikistan ya ce, an yi amfani da fasahar kasar Sin wajen gina gine-ginen 2, wadanda suka nuna salon gini na musamman na kasar Tajikistan. Wannan haduwar basira da aka yi shaida ce kan zumunci mai zurfi da aka samu a tsakanin kasashen Tajikistan da Sin.

Har ila yau, kasashen 2 sun gabatar da hadaddiyar sanarwa kan niyyarsu ta kulla huldar kawance ta hadin gwiwa kan manyan tsare-tsare na dukkan fannoni. (Bello Wang)