logo

HAUSA

Sin na maraba da kasashen da suka amince da “Ruhin Shanghai” da su shiga kungiyar SCO

2024-07-05 19:50:41 CMG Hausa

A yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda yayin da ta tabo batun amincewa kasar Belarus ta zama mamba a taron kolin kungiyar SCO na bana, jami’ar ta ce kasar Sin na maraba da karin kasashen da suka yarda da "Ruhin Shanghai" da su shiga kungiyar ta SCO.

Dangane da jibge makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango da Amurka ta yi a Philippines, Mao Ning ta ce matakin ya haifar da barazana ga tsaron yankin. Kuma kasar Sin ta bukaci kasashen da abin ya shafa da su dora muhimmanci kan muryoyin kasashen yankin, da kuma gyara kura-kurai cikin gaggawa.

Da ta tabo batun binciken da kungiyar EU ke yi kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin kuwa, Mao Ning ta ce, Sin na adawa da hakan, kuma a ko da yaushe tana ganin cewa, ya kamata a warware matsalolin tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata, ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Sai kuma batun rahoton kwamitin kare hakkin bil Adama na MDD, wanda ya amince da halartar kasar Sin, zagaye na hudu na duba batutuwan da suka shafi kare hakkin bil Adama na kasa, inda Mao Ning ta ce wannan ya nuna cewa, kasashen duniya sun amince da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin kare hakkin bil Adama, da kuma gudummawar da take bayarwa wajen kare hakkin bil Adama a matakin kasa da kasa.

Game da babban taron fasahohin kwaikwayon tunanin bil’adama ko AI na duniya, da kuma babban taron manyan jami’ai game da jagorancin fasahohin AI na duniya na shekarar 2024, wanda ake gudanarwa a birnin Shanghai na kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin na son daukar wannan taro a matsayin wata dama, ta yin hadin gwiwa tare da dukkan bangarori, domin inganta ci gaban fasahohin AI cikin lumana, da tsaro, da adalci da kuma tsari. (Safiyah Ma)