logo

HAUSA

Xi ya gudanar da babbar tattaunawa da shugaban Tajikistan

2024-07-05 21:16:14 CMG Hausa

Da yammacin yau Juma’a 5 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da babbar tattaunawa da takwaransa na Tajikistan Emomali Rahmon a fadar gwamnatin kasar dake birnin Dushanbe.

Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, Sin a shirye take ta raya cikakken tsarin kawance daga dukkanin fannoni tare da Tajikistan a sabon zamani, tare da gina al’umma mai makomar bai daya tsakanin Sin da Tajikistan daga mafari mai girma.

Kafin hakan, shugaba Xi ya gudanar da bikin mikawa shugaba Emomali Rahmon lambar karramawa ta abota, a fadar gwamnatin kasar dake birnin Dushanbe.  

Bayan da shugabannin 2 suka kammala tattaunawarsu, sun halarci bikin sa hannu kan wasu yarjeniyoyin hadin gwiwa, gami da ganawa da manema labaru tare, inda suka sanar da kulla huldar kawance da ta shafi manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu. (Saminu Alhassan)