logo

HAUSA

Yawan mutane da suka shiga da fita kasar Sin ya kai miliyan 278 a farkon rabin bana

2024-07-05 14:31:03 CMG Hausa

 

Hukumar shige da fice ta kasar Sin a yau ta fitar da alkaluman da suka nuna cewa, daga watan Jarairu zuwa Yuni, yawan mutanen da hukumar ta yi bincike a kansu ya kai miliyan 287, wanda ya karu da kashi 70.9% bisa makamancin lokaci na bara, daga cikinsu akwai baki miliyan 29.92.

A cikin wadannan lokuta, yawan bakin da suka shigo kasar Sin ta mabambantan tasoshin kwastam ya kai kimanin miliyan 14.63, wanda ya karu da kashi 152.7% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, baki fiye da miliyan 8.54 sun shiga ba tare da biza ba, wanda ya kai kashi 52% bisa na dukkannin baki, kuma ya karu da kashi 190.1% bisa na makamancin lokaci na bara. Dandalin ba da hidima mai suna “12367” ya amsa wayoyi sau miliyan 2.718 dake shafar kasashe da yankuna fiye da 100 a duniya. Mutane kashi 99.1% sun gamsu da hidimomin da aka samar musu. Hukumar ta yi kiyasin cewa, yawan bakin da za su zo yawon bude ido a nan kasar Sin zai ci gaba da karuwa a karshen rabin bana. (Amina Xu)