logo

HAUSA

Ziyarar Xi a Kazakhstan karo na biyar ta samu sakamako mai kyau

2024-07-04 20:11:34 CMG Hausa

Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda game da ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Kazakhstan, ta ce ziyarar cike take da abubuwa iri iri, kuma ta samu sakamako mai kyau, wanda hakan wani sabon mataki ne a tarihin ci gaban dangantakar kasashen biyu.

Game da harin da wasu dakaru dauke da makamai suka kai wa wani kamfanin Sin mai zaman kansa dake kasar Kongo(Kinshasa), wanda ya haddasa mutuwa da bacewar wasu Sinawa, Mao Ning ta bayyana cewa, bangaren Sin ya yi matukar Allah wadai da lamarin, yana kuma cudanya da bangaren Kongo(Kinshasa), don ganin an yi duk mai yiwuwa wajen ceto Sinawan da suka bata.

Don gane da yanayin da ake ciki a kudancin tekun kasar Sin kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa, kutsen da bangaren Philippines ya yi ba bisa ka'ida ba a yankin tudun Ren'ai na tsibiran Nansha na kasar Sin, ya yi matukar keta ikon mallakar yankunan kasar Sin. Kuma matakan tabbatar da doka da jami'an tsaron gabar tekun kasar Sin suka dauka na da ma'ana kuma suna bisa doka. 

Har ila yau, kasar Sin ta bukaci Philippines da ta daina tada-zaune-tsaye da tsokana, ta koma kan hanyar da ta dace ta warware bambance-bambance yadda ya kamata, ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Mao Ning ta kara da cewa, a cikin watanni biyar na farkon shekarar bana, sama da 'yan kasashen waje miliyan 12 ne suka shiga kasar Sin. Kaza lika, kasar Sin za ta ci gaba da inganta matakan taimakawa shige da fice, don kyautata damar yawon shakatawa ta kasar Sin ga abokai daga kasashen waje.  (Safiyah Ma)