logo

HAUSA

An kaddamar da cibiyar fasahar bibiyar albarkatun noma na shiyyar yammacin Afrika a tarayyar Najeriya

2024-07-04 10:42:35 CMG Hausa

 

Hukumar bunkasa binciken sararin samaniya ta Najeriya tare da hadin gwiwa da kwalejin nazarin harkokin kimiyya na kasar China sun kaddamar da cibiyar fasahar bibiyar rayuwar albarkatun noma na shiyyar yammacin Afrika a birnin Abuja dake tarayyar Najeriya.

An kaddamar da cibiyar ce ranar Talata 2 ga wata a Abuja yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin aikin gona da suka fito daga kasashen Afrika daban daban, inda suka yi muhawara a kan alfanun amfani da fasahar zamani wajen lura da amfanin gona tun daga shuka har zuwa lokacin girbi domin tabbatar da samun yalwataccen abinci a kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

A jawabin ta yayin taron daraktan lura da harkokin Afrika da yankin Asia a kwalejin kimiyya na kasar China Mrs Haihua Gong ta ce, tsarin amfani da fasahohin zamani wajen sanya ido a kan rayuwar sirrai da aka shuka domin abinci zai haifar da babban sauyi wajen samar da wadataccen abinci a kasashen Afrika baki daya.

“Wannan ingantaccen tsari dai zai iya baiwa kwararru a fannin kimiya na duniya damar samun wani kwarewa na musamman da suke bukata ta hanyar samar da gamsassun bayanai da za a rinka la’akari da su wajen sanin ingancin shuka da daukar matakin garkuwa ga duk wata annoba da za ta iya samun kayan amfanin gona kafin girbi da kuma bayan girbi.”

A nata jawabin babbar sakatariya a ma’aikatar kimiyya da fasahar kirkire-kirkire ta tarayyar Najeriya Mrs Esuabana Nko jaddada muhimmancin hadin kai ta yi wajen cimma nasarar wadata kasa da abinci, inda ta ce karancin abinci shi ne babbar matsalar da take addabar kasashen dake yammacin Afrika, wajibi ne kuma a hada hannun wuri guda domin shawo kan matsalar, inda ta ce samar da wannan tsari ta amfani da fasahohin zamani wajen lura da rayuwar amfanin gona babbar nasara ce da za ta kai ga Najeriya ga samun wadataccen abinci. (Garba Abdullahi Bagwai)