Xi: Gina gida guda na hadin kai da yarda da juna da kuma adalci
2024-07-04 20:40:45 CMG Hausa
A yau Alhamis, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kungiyar “SCO+” a birnin Astana na kasar Kazakhstan, ya ce ya kamata a gina gida guda na hadin kai da yarda da juna, da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da wadata da ci gaba, da kyakkyawar makwabtaka, da kuma adalci.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana maraba da dukkan bangarorin da za su yi amfani da tsarin tauraron dan Adam dake samar da hidimar taswira na Beidou na Sin, da kuma shiga aikin gina tashar nazarin kimiyya ta kasa da kasa ta duniyar wata.
Bugu da kari, ya kuma gana da shugaban kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan da babban sakataren MDD António Guterres a birnin na Astana. (Safiyah Ma)