logo

HAUSA

An watsa shirin “Bayanan Magabata Da Xi Jinping Yake So” ta kafofin yada labaran Kazakhstan

2024-07-03 09:58:14 CMG Hausa

 

An watsa shirin talabijin mai taken “Bayanan Magabata Da Xi Jinping Yake So”, ta kafofin yada labaran kasar Kazakhstan a jiya Talata, bayan da shugaban na Sin Xi Jinping ya isa birnin Astana, fadar mulkin kasar, don halartar taron majalisar gudanarwar kungiyar hadin gwiwar Shanghai ko (SCO) karo na 24 tare da ziyarar aiki a kasar.

Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ne ya tsara shirin na talabijin da harsuna daban daban, kuma daya daga manyan jaridun kasar Kazakhstan wato “Kazakhstanskaya Pravda”, ta wallafa sanarwa game da nuna shirin na CMG.

Jaridar ta bayyana shirin a matsayin wanda ya bayyana tsawon lokaci da kasar Sin ta shafe tana bude kofarta, da yin tafiya tare da dukkanin sassan ta fuskar raya al’adu. Kaza lika, ta fayyace yadda kasar Sin ke nacewa yayata akidar martaba mabambantan wayewar kai na duniya, da kwazon ta wajen ingiza zaman jituwa tsakanin mabambantan al’adu.

Har ila yau, shirin ya yi wa masu kallo daga kasashe da suka shiga shawarar “ziri daya da hanya daya” irin su Kazakhstan karin haske, game da mahangar shugaba Xi, don gane da gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama. (Saminu Alhassan)