An gudanar da taron tattaunawa na kafofin watsa labarai na kasashen Sin-SCO a Astana
2024-07-03 20:08:28 CMG Hausa
A gabannin taron shugabannin kasashen mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO karo na 24, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya gudanar da taron tattaunawa na kafofin watsa labarai na kasashen Sin-SCO a Astana, fadar mulkin Kazakhstan.
A cikin jawabinsa, shugaban CMG, Shen Haixiong ya ce, CMG na fatan yin aikin tukuru tare da kafofin watsa labarai na kasashen SCO, don inganta ci gaban SCO tare bisa kwararan matakai, ta yadda za a ba da gudummawa ga inganta gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama.(Safiyah Ma)