logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya isa birnin Astana na kasar Kazakhstan

2024-07-02 14:49:55 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Astana na kasar Kazakhstan Yau Talata.

Yayin da jirgin sama na musamman dake dauke da shugaba Xi Jinping ya shiga sararin samaniyar kasar Kazakstan, jiragen saman yaki na kasar 2 sun yi masa rakiya. Sa’an nan, shugaban kasar Kassym-Jomart Tokayev shi da kansa ya tarbe Xi Jinping a filin saukar jiragen sama na kasar.

A safiyar yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing don halartar taron majalisar gudanarwar kungiyar hadin gwiwar Shanghai (SCO) karo na 24 a birnin Astana, da kuma ziyarar aiki a kasashen Kazakhstan da Tajikistan bisa gayyatar da Shugaba Kassym-Jomart Tokayev na jamhuriyyar Kazakhstan da Shugaba Emomali Rahmon na jamhuriyyar Tajikistan suka yi masa. (Yahaya)