Kasar Habasha ta yaba da rawar da Huawei ke takawa wajen bunkasa hazaka a fannin ICT
2024-07-02 13:33:04 CMG Hausa
Gwamnatin kasar Habasha ta yabawa katafaren kamfanin fasaha na kasar Sin Huawei bisa irin gudummawar da yake bayarwa ga matasan kasar wajen bunkasa fasahar sadarwa ko ICT a takaice.
Solomon Soka, karamin ministan ma'aikatar kwadago da fasaha na kasar Habasha ne ya bayyana hakan a yayin wani taron da aka shirya wa daliban kasar Habasha da za su halarci shirin horaswa na “Huawei Seeds for the Future 2024” a Morocco daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Yuli, a cewar Huawei Habasha a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.
Ministan ya yaba da rawar da kamfanin Huawei ke takawa wajen bunkasa hazaka a kasar dake gabashin Afirka, ministan ya ce irin wadannan shirye-shiryen horaswa na ICT na taimaka wa matasan kasar wajen bunkasa fasaharsu da iliminsu a wannan fanni. Ya ce irin wadannan shirye-shiryen horaswa masu habaka fasaha za su kara kyautata hanyoyin samun sana’a ga matasa tare da bude musu kofofin sabbin guraben ayyukan yi.
Dalibai 10 daga jami'o'in gwamnati takwas na kasar Habasha za su halarci shirin horaswa na Huawei Seeds for the Future 2024, wanda zai hada dalibai kusan 160 daga kasashen Afirka 18. (Yahaya)