logo

HAUSA

An kaddamar da yankin hakar danyen mai ta kasan teku bisa tsarin kare muhalli a kudancin Sin

2024-07-02 19:16:08 CMG Hausa

A jiya Litinin ne aka kaddamar da yankin hakar danyen mai ta kasan teku, bisa tsarin kare muhalli, a zirin teku na Beibu dake kudancin kasar Sin.

A cewar kamfanin hakar danyen mai ta kasan teku na Sin, wannan ne karon farko da Sin ta bude cikakken tsarin hakar danyen mai bisa matakan kare muhalli, tare da dora muhimmaci ga karkata ga salon rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayi a fannin bunkasa makamashin kasar.

Ya zuwa shekarar 2026, an yi hasashen kaiwa kololuwar aiki da mahakar danyen man, inda za ta kai ga rika samar da danyen mai har ganga  18,100 a kowace rana. (Saminu Alhassan)