logo

HAUSA

An Wallafa Makalar Da Xi Jinping Ya Rubuta Mai Taken “Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Kazakhstan Cikin Hadin Kai”

2024-07-02 15:05:11 CMG Hausa

An wallafa makalar da Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken “Bude sabon babin huldar Sin da Kazakhstan cikin hadin kai” a jaridar “Kazakhstanskaya Pravda” da kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa na Kazakhstan a yau Talata yayin da yake ziyarar aiki a kasar. A cikin makalarsa, ya bayyana fatansa na hadin kai da takwaransa na kasar Kassym-Jomart Kemeluly Tokayev a ziyararsa na wannan karo, don habaka dankon zumuncin kasashen biyu da zurfafa hadin gwiwarsu a dukkanin fannoni, da ma gabatar da sabbin tsare-tsaren raya huldar kasashen biyu nan gaba, kana da ingiza dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fanonni tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

Wannan ziyara ta kasance karo na 5 da shugaba Xi Jinping ya yi a kasar Kazakhsatan a wa’adinsa.

Wani muhimmin aiki na daban a ziyarar Xi Jinping a wannan karo shi ne halartar taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai. Ya yi imani cewa, ba shakka za a cimma nasara a taron da za a gudanar a Astana, fadar mulkin kasar karkashin kokarin bangarori daban-daban, da ma habaka zumuncin mambobin kungiyar, ta yadda za a bude wani sabon babin hadin gwiwarsu. (Amina Xu)