logo

HAUSA

Sin za ta karbi ragamar shugabancin SCO daga shekarar 2024 zuwa 2025

2024-07-01 20:05:48 CMG Hausa

 

A yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda game da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Kazakhstan don halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, ta ce shugaba Xi Jinping zai yi musanyar ra'ayi mai zurfi da shugabannin kasashen dake halartar taron, don gane da zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban a karkashin sabon yanayi, da kuma manyan batutuwan duniya da na yankuna a halin da ake ciki. Jami’ar ta ce bayan taron, Sin za ta karbi ragamar shugabancin kungiyar SCO daga shekarar 2024 zuwa 2025.

Game da bikin tunawa da cika shekaru 70, da fitar da ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana, wanda Sin ta gudanar a baya bayan nan, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da dukkan bangarori, wajen aiwatar da babban ra'ayin da aka cimma a yayin bikin, da sa kaimi ga ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana, da kuma inganta gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin bil'adama.

Game da mu'amala da hadin gwiwa a bangaren nazarin sararin samaniya tsakanin Sin da Amurka, Mao Ning ta ce, kofar gwamnatin Sin a bude take a wannan fage. To sai dai kuma ga alama Amurka, ta manta da wanzuwar dokokin ta na cikin gida, irin su "Wolf Clause", don haka babu tabbas, kan ko gwamnatin Amurka za ta ba da izinin shiga mu'amala, da hadin gwiwa tare da Sin tsakanin masana kimiyya da cibiyoyin da abun ya shafa na kasarta.

Dangane da rahoton da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, na yin kalamai marasa ma’ana kan harkokin addinai na Sin, Mao Ning ta ce, Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta gaskiya, ta gyara kuskurenta, ta kuma daina amfani da batutuwan addini, wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin.(Safiyah Ma)