Sin ta fadada damar cin gajiyar bincike kan ikon mallakar fasaha tare da Iceland da Masar
2024-07-01 21:02:48 CMG Hausa
Sin ta fadada shirin ta na samar da damar cin gajiyar bincike kan ikon mallakar fasaha ko PPH tare da kasashen Iceland da Masar, matakin da zai ba da zarafin cin gajiya cikin sauki daga hidimomin bincike ga masu neman izinin mallakar fasaha.
Hukumar kasar Sin mai lura da kare ikon mallakar fasahohi ko CNIPA, da takwarorinta na Iceland da Masar, sun amince da aiwatar da shirin gwaji na PPH cikin shekaru biyar, tun daga 1 ga watan Yulin nan zuwa 30 ga watan Yunin 2029. (Saminu Alhassan)