Xi Jinping zai halarci taron shugabannin kasashe mambobin SCO karo na 24
2024-06-30 16:20:09 CMG Hausa
Bisa labarin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar, daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci taro karo na 24 na shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, wanda za a gudanar a birnin Astana, fadar mulkin Kazakhstan.
Kaza lika, shugaba Xi zai gudanar da ziyarar aiki a Kazakhstan da Tajikistan, bisa gayyatar da shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, da na Tajikistan Emomali Rahmon suka yi masa. (Safiyah Ma)