logo

HAUSA

Xi ya aike da wasikar taya murnar kammalawa da bude gada kan teku tsakanin Shenzhen da Zhongshan

2024-06-30 15:57:31 CMG Hausa

A yau Lahadi ne aka kammala, tare da bude gada kan teku da ta hada biranen Shenzhen da Zhongshan, kuma albarkacin bikin budewar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon fatan alheri, tare da mika gaisuwa ta hakika, ga daukacin jami’ai da suka ba da gudummawa, wajen tsarawa da kuma gina hanyar.

Cikin sakon na sa, shugaba Xi ya ce wannan gada da ta hada biranen Shenzhen da Zhongshan, wani babban aiki ne na raya hada hadar sufuri a yankin mashigin Guangdong da Hong Kong da Macao, wanda ya biyo bayan kammala babbar gadar Hong Kong zuwa Zhuhai zuwa Macao. Ya ce aikin ya cimma nasarar haye manyan wahalhalun gine gine na duniya, da kafa tarihi a sassa daban daban na fasahar gine gine. Ya ce abu na gaba shi ne tabbatar da ingancin gadar yadda ya kamata, da yayata hade kasuwannin dake babban zirin na Guangdong, da Hong Kong da Macao.

Gadar da ta hade biranen Shenzhen da Zhongshan, na da tsayin kusan kilomita 24, kuma ita ce irinta ta farko da ta hade yankin teku, da gadoji, da tsibirai, da hanyoyin karkashin ruwa. Bayan bude ta, adadin lokacin da ake bukata na tafiya daga Shenzhen zuwa Zhongshan, zai ragu daga kusan sa’o’i 2 a yanzu zuwa mintuna 30 kacal. (Saminu Alhassan)