Shugaban bankin duniya ya yi tsokaci kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin
2024-06-29 16:46:44 CMG Hausa
Kwanan baya, shugaban bankin duniya Ajay Banga ya bayyana a wata hirar da ya yi da wakiliyar gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG cewa, kasar Sin mai yawan al’umma biliyan 1.4, tana taka rawar gani wajen ci gaban tattalin arzikin duniya. Kana, kyautatuwar tattalin arzikin kasar Sin na da matukar muhimmanci ga sauran kasashen duniya.
Kasar Sin ta sanya burin samun bunkasuwa kusan kashi 5 cikin kashi 100 a wannan shekara ta 2024. Game da wannan batu, Ajay Banga ya ce, duba ga girman tattalin arzikin kasar Sin, kashi 5 cikin kashi 100 adadi ne mai armashi. Tattalin arzikin kasar Sin ya sha bamban da yadda yake yau sama da shekaru 20 ko 30 da suka gabata. Kasar Sin na sauya tattalin arzikinta don nan gaba. Kwalliya ta biya kudin sabulu game da tsarin bunkasuwar tattalin arzikin Sin na goman shekaru da suka gabata. Yanzu kasar Sin na mai da hankali kan tsarin bunkasa tattalin arziki na nan gaba. Wannan na bukatar kirkire-kirkiren fasahohi, da masana’antu mara gurbata muhalli, da bunkasa bukatun jama’a. Wannan bunkasuwa ce ta daban, kuma sauyin zai dauki lokaci. Amma ko da ci gaban tattalin arzikin Sin ya kasance kashi 5 cikin kashi 100 kawai, gudummawar da Sin ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya ya kai kashi 30 cikin kashi 100. (Yahaya)